Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage yanke hukunci kan bukatar tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, na cewa babu wata hujjar da za ta sa a ci gaba da shari’ar da ake yi masa zuwa ranar 26 ga Oktoba, 2026.

Shari’ar ta shafi wata hira da El-Rufai ya yi da Arise TV a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, inda aka ce ya amsa cewa ya saurari wasu tattaunawar waya da ta shafi mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Ana tuhumar El-Rufai da laifuka biyar da suka shafi dokokin laifukan yanar gizo da sadarwa.

Lauyoyinsa sun ce masu gabatar da ƙara ba su gabatar da isasshiyar hujjar da za ta tilasta masa shiga matakin kare kansa ba, yayin da DSS ke dogaro da kalaman da aka jingina masa da kuma shaidar wasu shaidu.

Hukuncin kotun zai bayyana ko za a ci gaba da shari’ar zuwa matakin kare kai ko kuma za a dakatar da ƙarar a wannan mataki.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *