Kasashe takwas masu rinjayen Musulmi sun bukaci Isra’ila ta cika alkawuran da ta dauka karkashin matakin farko na shirin tsagaita bude wuta a Gaza, musamman ta hanyar ba da damar shigar da agajin jin kai cikin gaggawa da ba tare da tsaiko ba.

Ministocin harkokin wajen Turkiyya da Masar da Indonesia da Jordan da Pakistan da Qatar da Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwa kan ci gaba da wahalhalun jin kai da Falasdinawa ke fuskanta a Gaza, tare da yin kira da a dakatar da duk wani take yarjejeniyar.

Irin wannan hadin gwiwa tsakanin kasashen takwas sun dade suna bayyana matsayinsu kan batun Gaza.

Kasashen sun kuma yi watsi da duk wani mataki da zai kai ga korar Falasdinawa ko tilasta musu barin gidajensu, tare da cewa bai kamata a sauya yanayin yankin Falasdinawa ta fuskar kasa ko al’umma ba.

Sun kuma bukaci Amurka ta ci gaba da taka rawa wajen tabbatar da aiwatar da shirin, tare da jaddada cewa Gaza ta kasance wani bangare na yankin Falasdinawa, yayin da ake neman hanyar da za ta kai ga kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *