Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su shirya juyin juya hali, yana zargin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙwace ikon ɓangaren shari’a da kuma tauye ’yancin kafafen yaɗa labarai.
Sowore ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi ikirarin cewa an yi wa ɓangaren shari’a katsalandan, an mamaye manyan kafafen yaɗa labarai, sannan ana kai hare-hare kan ’yan siyasar adawa.
- Peter Obi ya kalubalanci Tinubu kan yadda aka kashe tiriliyan 15.8 na tallafin mai
- Magoya bayan APC sun gudanar da gangamin goyon bayan sake zaɓen Tinubu a Yobe
- Gwamnatin tarayya ta hana NTI Kaduna karɓar sababbin ɗalibai a 2026
Ya ce waɗannan abubuwa sun nuna cewa Tinubu ba ya shirin gudanar da zaɓe yadda ya kamata, a cewarsa, don haka ya kamata ’yan Najeriya su shirya wani sauyi ta hanyar juyin juya hali.
Sai dai Sowore bai bayar da ƙarin bayanai ko hujjoji a cikin saƙon nasa da ke tabbatar da zarge-zargen da ya yi kan gwamnati ba.
Kiran nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027, inda jam’iyyun adawa da masu ruwa da tsaki ke bayyana ra’ayoyinsu kan yanayin siyasar ƙasar.