Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasar na shirin sake taka muhimmiyar rawa a fannin binciken sararin samaniya da bunƙasa kimiyya da fasaha.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake ziyarar cibiyar binciken sararin samaniya ta NASA da ke Kennedy Space Center.
- Sowore ya zargi Tinubu da shirin hana gudanar da sahihin zaɓe a Najeriya
- Magoya bayan APC sun gudanar da gangamin goyon bayan sake zaɓen Tinubu a Yobe
Ya ce kasancewa ɗan Amurka na nufin gadon tarihin manyan masu bincike, matafiya, masu ƙirƙira da masana fasaha da suka bayar da gudummawa wajen ci gaban ƙasar.
Shugaban ya ce Amurka a shirye take ta sake tabbatar da ƙarfinta, duk da masu shakkar ƙarfinta, ta hanyar cimma wasu manyan nasarori a fannin binciken sararin samaniya.
A kalamansa, ƙasar na da burin ɗaukar wasu manyan matakai da za su amfani bil’adama baki ɗaya.
