Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, bisa rasuwar mahaifinsa, Elhadji Tiani Hassane, wanda ya rasu kwanan nan yana da shekara 110 a duniya.

A cikin saƙon ta’aziyyar da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya ce gwamnatin Najeriya da al’ummarta na tare da gwamnatin Nijar da jama’arta a wannan lokacin jimami.

Shugaban ya bayyana marigayin a matsayin mutumin da ya rayu tsawon lokaci mai albarka, tare da bayar da gudummawa mai ɗorewa ga rayuwar al’ummarsa.

Ya kuma buƙaci Janar Tiani da iyalansa su yi haƙuri, tare da samun ƙwarin gwiwa daga kyawawan halayen da mahaifinsa ya bari, musamman imani, mutunci da riƙon amana.

Tinubu ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya jiƙan marigayin, ya ba shi Aljannatul Firdausi, sannan ya ba iyalansa da sauran waɗanda ya bari haƙurin jure wannan rashi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *