Jam’iyyar ADC ta buƙaci ’yan Najeriya su yi koyi da masu kaɗa ƙuri’a a Amurka, inda ta ce sun nuna rashin amincewarsu da jam’iyyar Republican mai mulki sakamakon hauhawar farashin man fetur da tsadar rayuwa.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, inda ta ce tsadar rayuwa da ƙarfin da jama’a ke da shi na sayen muhimman kayayyaki za su taka muhimmiyar rawa a zaɓen Najeriya mai zuwa.

ADC ta ce yayin da farashin man fetur ya ƙaru da kusan kashi 37 cikin ɗari a wasu jihohin Amurka, farashin fetur a Najeriya ya tashi da kusan kashi 570 cikin ɗari tun bayan cire tallafin mai a watan Mayun 2023.

Jam’iyyar ta ce farashin lita ya tashi daga Naira 238.11 a watan Mayun 2023 zuwa Naira 1,596.25 a watan Mayun 2026.

Ta bayyana cewa wannan ƙarin farashi ya wuce ƙididdigar tattalin arziki kawai, domin a cewarta, ya sa sufuri ya yi tsada, farashin abinci ya ƙaru, sannan ƙananan sana’o’i suka shiga mawuyacin hali.

Jam’iyyar ta zargi gwamnatin APC da Shugaba Bola Tinubu da aiwatar da manufofin da suka jefa gidajen ’yan Najeriya cikin matsin rayuwa.

Jam’iyyar ta ce yayin da gwamnatin ke ci gaba da neman ’yan ƙasa su yi haƙuri da sadaukarwa domin samun kyakkyawar makoma, ba ta bayyana yadda cire tallafin mai zai amfani talakawa ba bayan fiye da shekaru uku.

Ta kuma buƙaci gwamnati ta yi bayani kan matakan da za ta ɗauka domin rage kuɗin man fetur, wutar lantarki, abinci da sufuri.

ADC ta ce darasin da take ganin ya kamata Najeriya ta koya daga zaɓen Amurka shi ne cewa dole ne gwamnati ta yi wa jama’a bayani kan tasirin manufofinta na tattalin arziki.

Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi la’akari da halin tsadar rayuwa yayin zaɓen da ta ambata a matsayin wanda za a gudanar ranar 16 ga Janairu, tare da jaddada matsayinta na adawa da jam’iyyar APC mai mulki.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *