Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta soke dukkan guraben karatun da Cibiyar Horar da Malamai ta Ƙasa (NTI) da ke Kaduna ta bayar na shekarar karatu ta 2026, ciki har da shirye-shiryen NCE da digiri.

Haka kuma, ma’aikatar ta umarci cibiyar da ta dakatar da duk wata alaƙa da jami’o’i wajen gudanar da shirye-shiryen digiri.

Ta kuma gargaɗi ɗalibai masu neman gurbin karatu, iyaye da sauran jama’a da kada su nemi shiga shirye-shiryen da abin ya shafa.

A cikin sanarwar da ta fitar ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, ma’aikatar ta ce NTI ba ta da izinin bayar da takardar shaidar NCE ko digiri na jami’a.

Ta bayyana cewa matakin ya shafi karatun cikakken lokaci, na wucin gadi da kuma tsarin karatu ta nesa (DLS), tare da hana cibiyar karɓar sababbin ɗalibai ko kuɗin makaranta.

Ma’aikatar ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon karya ƙa’idojin gudanarwa da Ministan Ilimi ya fitar a ranar 12 ga Satumba, 2025.

Ta bayyana cewa karɓar ɗalibai a shirye-shiryen NCE dole ne ya bi ƙa’idojin Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) da kuma Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (NCCE).

Sai dai ma’aikatar ta ce ta ɗauki matakan kare ɗaliban da suka riga suka fara karatu a cibiyar, inda ta umarci NCCE da ta tantance shirye-shiryen NCE II zuwa IV na karatun nesa da cibiyoyin karatun da ke faɗin shiyyoyin siyasa shida na ƙasar, domin tantance ɗaliban da za su iya kammala karatunsu bisa sakamakon tantancewar da sauran ƙa’idoji.

Ta ƙara da cewa aikin NTI na doka shi ne horar da malamai, sake horar da su da kuma inganta ƙwarewarsu a kai a kai.

Ma’aikatar ta buƙaci jama’a su tabbatar da sahihancin shirye-shiryen karatu da amincewar hukumomin da abin ya shafa kafin neman gurbi ko biyan kuɗi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *