Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya bayanin yadda gwamnatinsa ta yi amfani da kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur da kuma bashin da ta karɓa tun bayan hawanta mulki.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin saƙon da ya wallafa mai taken “Good Day, Mr President”, inda ya taya shugaban ƙasar murnar kwana ɗaya a jihar Akwa Ibom, wadda ke ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ba su cikin Legas da Abuja.

Ya ce yana fatan ziyarar za ta ƙarfafa Tinubu ya kai ziyara sauran jihohin ƙasar domin ganawa da jama’a tare da bayyana abin da gwamnatinsa ta cimma da kuɗaɗen da ta samu, ciki har da Naira tiriliyan 15.8 da aka ce an samu daga cire tallafin mai, sama da dala biliyan 100 na bashin da aka karɓa da ƙarin kuɗaɗen shiga daga haraji.

Tsohon gwamnan Anambbra ya ce ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin adadin mutanen da aka fitar daga kangin talauci, yaran da aka mayar makaranta, da kuma cibiyoyin kula da lafiya matakin farko da aka gina kuma suke aiki.

Obi ya kuma buƙaci gwamnati ta bayyana irin ci gaban da aka samu wajen samar da wutar lantarki da kuma tsaro, yana mai cewa ƙasar na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen da matsalar ta’addanci ta fi shafa a duniya.

Ya jaddada cewa ’yan Najeriya sun cancanci samun amsoshi kan yadda aka yi amfani da dukiyoyin ƙasar da aka damƙa wa gwamnati, yana mai cewa sabon Najeriya da yake fata za a gina shi ne bisa riƙon amana, gaskiya da kuma sakamakon da za a iya aunawa a rayuwar al’umma.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *