Najeriya da Turkiyya sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin sadarwa, bunƙasa kafafen yaɗa labarai, musayar al’adu da yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da bayanan da aka ƙirƙira da gangan.

Hakan na cikin sakamakon ganawar da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma na Najeriya, Mohammed Idris, ya yi da shugaban Hukumar Sadarwa ta Turkiyya, Farfesa Burhanettin Duran, a birnin Istanbul ranar Asabar, yayin taron TRT World Forum.

Ministan ya gode wa gwamnatin Turkiyya bisa gayyatar da ta yi wa Najeriya, tare da yaba mata kan ƙara faɗaɗa hulɗarta da Afirka, musamman Najeriya.

Ya kuma yaba wa gidan rediyo da talabijin na TRT bisa faɗaɗa ayyukansa a Afirka, ciki har da shirye-shiryensa na Hausa da horar da ’yan jaridun Najeriya.

Mohammed Idris ya bayyana shirye-shiryen Najeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa da Turkiyya wajen yaƙi da labaran ƙarya, yaɗa bayanan da ba daidai ba da kuma amfani da fasahar basirar wucin gadi ta hanyar da za ta cutar da al’umma.

Ya ce waɗannan abubuwa na barazana ga amincewar jama’a, zaman lafiya da tsaron ƙasashe.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar ƙasashen duniya da wayar da kan jama’a kan yadda ake tantance bayanai, tare da bayyana cewa Najeriya ce mai masaukin baki ga Cibiyar Yaɗa Labarai da Ilimin Fahimtar Bayanai ta Duniya, wadda ke ƙarƙashin rukunin cibiyoyin UNESCO na Category 2.

A nasa ɓangaren, Farfesa Duran ya bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa, tare da nuna goyon bayan Turkiyya ga yarjejeniyoyin fahimtar juna tsakanin hukumomin sadarwa da kafafen yaɗa labaran gwamnati na ƙasashen biyu, ciki har da NTA, FRCN, NAN da VON.

Duran ya kuma gayyaci Najeriya ta halarci taron koli na shida kan Sadarwar Dabarun Ƙasa da Ƙasa, wanda za a gudanar a Istanbul a watan Janairun 2027.

Jami’an biyu sun amince da ci gaba da tattaunawa da ƙarfafa haɗin gwiwar hukumominsu domin bunƙasa musayar shirye-shirye, horar da ma’aikata da fasaha, tare da amfani da sadarwa da diflomasiyyar al’adu wajen inganta zaman lafiya da ci gaba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *