Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta sanar da cewa za ta gudanar da addu’a ta musamman domin zaman lafiya da tsaro da ci gaban Najeriya.
Za a gudanar da addu’ar ne ranar Laraba, 30 ga Satumba 2026, a harabar Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, daga ƙarfe 4:30 na yamma zuwa 6:30 na yamma.
Majalisar NSCIA ta ce addu’ar za ta ba Musulmi damar haɗuwa domin roƙon Allah Ya ba Najeriya da al’ummarta jagoranci da kariya da zaman lafiya da albarka.
- NCAA ta umarci kamfanin Air Peace ya biya fasinjojin jirgin Lagos-Enugu diyya
- Kotu ta dage yanke hukunci kan karar El-Rufai zuwa 26 ga Oktoba
A ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, majalisar za ta kuma gudanar da Babban Taron Majalisar a wurin, wanda zai fara da ƙarfe 10 na safe.
NSCIA ta ce Babban Taron shi ne mafi girman matakin yanke shawara na majalisar, kuma zai haɗa wakilan majalisun harkokin Musulunci na jihohi 36 da Abuja da jami’an gwamnati Musulmi da ƙungiyoyin Musulunci da sauran manyan mutane, domin tattauna batutuwan da suka shafi Musulmi da ƙasar baki ɗaya.
Majalisar ta kuma yi kira ga Musulmi a faɗin Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a ga zaman lafiya da haɗin kai da tsaro da shugabanci nagari da ci gaba mai ɗorewa a ƙasar.