Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Jihar Neja, ta jajanta wa Gwamna Mohammed Umaru Bago da al’ummar jihar bisa rasuwar matasa 37 masu haƙar ma’adinai da suka mutu yayin da suke tsare a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC).
Mataimakin Shugaban CAN na Jihar Neja, Rev. Joshua Markus Rikoto, wanda ya wakilci Shugaban ƙungiyar kuma Bishop na Katolika ta Kontagora, ya jagoranci tawagar zuwa gidan gwamnatin jihar da ke Minna domin mika sakon ta’aziyya.
CAN ta bayyana lamarin a matsayin babban bala’i mai cike da raɗaɗi, tare da kira da a gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar matasan.
- Kotu ta dage yanke hukunci kan karar El-Rufai zuwa 26 ga Oktoba
- NSCIA za ta gudanar da addu’ar ƙasa baki ɗaya a Abuja ranar 30 ga Satumba
CAN Ta kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa kafa kwamitin bincike kan lamarin.
Ƙungiyar ta yi kira ga iyalan waɗanda suka mutu da mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankali tare da bin doka yayin da ake gudanar da bincike.
Da yake mayar da martani, Gwamna Bago ya ce mutuwar matasan 37 lamari ne mai matuƙar tayar da hankali wanda bai kamata a yi watsi da shi ba.
Ya tabbatar wa CAN cewa gwamnatinsa za ta bibiyi lamarin har zuwa ƙarshe, domin gano gaskiyar abin da ya faru.