Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar NDC, watanni uku bayan ya fice daga ADC sakamakon rikicin cikin gida da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Lawal, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ADC, ya yi murabus daga jam’iyyar yana zargin an karkatar da tsarin zaɓen fidda gwani domin bai wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, tikitin takarar shugaban ƙasa.
- NSCIA za ta gudanar da addu’ar ƙasa baki ɗaya a Abuja ranar 30 ga Satumba
- CAN ta nemi a binciki mutuwar matasa 37 masu haƙar ma’adinai a Neja
A watan Yunin 2026, an ruwaito cewa Lawal na shirin komawa jam’iyyar NDC bayan ficewarsa daga ADC, yayin da rahotanni daga baya suka tabbatar da cewa ya shiga jam’iyyar.
Komawar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, NDC ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke shirin ƙarfafa tsarinta gabanin zaɓen 2027.