Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta kare duk wani jami’in da bincike ya gano yana da hannu wajen mutuwar mutane 37 da suka rasu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja ba.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kwamitin bincike mai zaman kansa mai mambobi 10 a Abuja, bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kwamitin zai binciki yadda aka kama da tsare mutanen, tare da gano musabbabin mutuwarsu ta hanyar binciken lafiya da na kimiyya.

Haka kuma kwamitin zai tantance ko sakaci ko rashin ɗa’a ko haɗin baki ko karya aikin da ya rataya kan jami’ai ya faru.

Ministan ya umarci NSCDC da sauran jami’an da abin ya shafa su miƙa dukkan takardu da hujjojin da suka shafi lamarin.

Ya kuma gargadi duk wanda ya lalata ko ɓoye hujja, tsoratar da shaidu ko ƙoƙarin hana binciken gudanar da aikinsa cewa za a ɗauki matakin doka a kansa.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin tsohon babban jami’in DSS, Jonathan Kure, zai fara aiki nan take kuma ana sa ran zai gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *