Gwamnatin Jihar Legas ta ce tana ƙoƙarin amfani da ƙarin haɗin gwiwar duniya da jihar ke samu wajen jawo sabbin damar zuba jari da haɗin gwiwar da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikinta.
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana hakan yayin taron Global Africa Business Initiative a New York, inda ya ce Legas na buƙatar sauya haɗin gwiwar duniya zuwa ayyukan more rayuwa da damar tattalin arziki da za su amfani mazauna jihar.
- Shugabannin Gulf za su matsa wa Trump kan hanyar kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya
- NDC na shirin ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen 2027
Ya ce daga cikin abubuwan da gwamnatin ke bai wa fifiko akwai inganta harkokin sufuri da faɗaɗa kiwon lafiya da kuma samar da yanayin da zai bai wa matasa masu sana’o’i damar bunƙasa.
Gwamnan ya ce Legas za ta ci gaba da gina hulɗa da masu zuba jari da sauran abokan hulɗa na duniya, yana mai cewa jihar a shirye take ta karɓi harkokin kasuwanci tare da tabbatar da cewa irin waɗannan damar sun haifar da amfani ga al’ummar jihar.