Mataimakin Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) mai kula da ɓangaren tacewa da rarraba man fetur, Dakta Mumuni Dagazau, ya bukaci manyan da ƙananan ’yan kasuwar man fetur su rungumi haɗin gwiwa da haɗa kamfanoni domin ƙarfafa kasuwancinsu da rage kuɗin gudanarwa.

Dagazau ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa a makon OTL Africa Downstream Energy Week karo na 20 da aka gudanar a Legas, inda ya ce daidaitattun manufofin gwamnati da zuba jari a kayayyakin more rayuwa na man fetur sun taimaka wajen jawo hankalin masu zuba jari da samar da damar haɗin gwiwa a ɓangaren.

Ya ce NNPC na zuba jari wajen inganta bututun jigilar man fetur domin tabbatar da wadatar kayayyakin mai, tare da saka hannun jari a motocin iskar gas ta CNG, motocin lantarki da kuma iskar gas ta LPG.

Ya ƙara da cewa daidaituwar kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta taimaka wajen ƙara shigo da masu zuba jari.

Dagazau ya jaddada muhimmancin samar da gasa mai kyau a kasuwar man fetur, yana mai ba da shawarar amfani da hanyoyin rage kuɗin gudanar da kasuwanci, ciki har da jigilar iskar gas ta CNG da manyan motoci.

Ya kuma bukaci ’yan kasuwa su fi mayar da hankali kan haɗin gwiwa da haɗa kamfanoni maimakon sayen kamfanonin wasu.

An gudanar da taron OTL Africa Downstream Energy Week na bana daga ranar 25 zuwa 30 ga Oktoba, 2026, a otal ɗin Lagos Oriental da ke tsibirin Victoria a Legas.

Taron, wanda ke haɗa masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur daga faɗin Afirka, ya gudana ne ƙarƙashin taken “Tabbatar da Samar da Makamashi, Wadata Ga Kowa.”

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *