Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi kira ga shugabannin siyasa da ’yan Najeriya da su sauya daga siyasar neman gata da nuna ƙabilanci zuwa siyasar ɗaukar nauyi, ƙarfafa hukumomi da samar da ayyukan da za su amfani jama’a.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, yayin da aka karrama shi da shigar da shi cikin jerin fitattun mutane na Idoma Hall of Fame, a wani taro da aka gudanar a Abuja mai taken “Jama’a, Siyasa da Fafutukar Ƙarfi a Najeriya: Neman Daidaito da Adalci.”

Ministan ya ce adalci na gaskiya yana nufin bai wa kowane ɗan Najeriya damar shiga harkokin ƙasa, amfana da ayyukan hukumomin gwamnati da kuma samun tabbacin cewa ƙasa ba ta fi karkata ga wata ƙabila ko rukuni fiye da wani ba.

Ya yi gargaɗin cewa bai kamata a mayar da adalci gasa kan rabon mukamai bisa ƙabila ko sauya waɗanda ke riƙe da madafun iko kawai ba, inda ya ce wakilcin ƙungiyoyi a gwamnati yana da muhimmanci, amma bai kamata a fifita shi a kan ƙwarewa da ingancin aikin da ake yi ba.

Wike ya ce ya kamata ’yan Najeriya su daina tambayar lokacin da nasu za su samu mulki da rabonsu na arzikin ƙasa kawai, su fara tambayar abin da za su yi da mulki idan sun samu, da kuma yadda za a faɗaɗa arzikin ƙasar tare da raba shi cikin adalci.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa tantance shugabanni bisa ayyukan raya ƙasa da ingancin hidimar da suke bayarwa, maimakon dogaro da hayaniyar siyasa, inda ya yi nuni da ayyukan more rayuwa a tsakiyar birnin Abuja da garuruwan da ke kewaye da shi a matsayin abin da ya ce ya nuna irin yadda ake gudanar da mulki a ƙarƙashinsa.

Ministan ya ƙara da cewa yawan kuɗaɗen da yanzu ke isa ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ya sa ya kamata ’yan ƙasa su riƙa neman bayanin yadda ake amfani da kuɗaɗen daga gwamnoninsu da shugabannin ƙananan hukumomi, ba wai su ɗora dukkan alhakin gudanar da mulki a kan gwamnatin tarayya kaɗai ba.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin shirya taron na Idoma Hall of Fame, Paul Harris Ogbole, ya ce an ƙirƙiri shirin laccoci na shekara-shekara ne domin adanawa da kiyaye tarihin nasarorin ’yan asalin Idoma da kuma karrama wasu fitattun mutane daga wajen al’ummar da suka bayar da gudunmawa ga ci gabanta.

Shi kuwa mai kwanda ya shirya taron, Injiniya Agaba Ikwue, ya bayyana cewa an tsara kafa gidan tarihi na zahiri da na zamani ta intanet domin adanawa da sauƙaƙa samun tarihin al’ummar Idoma, nasarorinsu, al’adunsu da gudunmawar da suka bayar ga ci gaban al’umma.

Babban limamin cocin Dunamis, Fasto Paul Enenche, da matarsa Becky Enenche ne suka jagoranci buɗe littafin tattara tarihin waɗanda aka karrama a Idoma Hall of Fame.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *