Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gabatar da matsayin Najeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 da ke gudana a New York, inda ya yi kira da a sake fasalin tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Shettima ya ce Afirka ba za ta ci gaba da kasancewa a gefe wajen yanke manyan shawarar da suka shafi duniya ba, yana mai cewa bai dace tsarin rabon iko na shekarar 1945 ya ci gaba da kasancewa tushen tsarin duniya a shekarar 2026 ba.
- Gwamna Aliyu ya ce ba za su sassauta wa ’yan bindiga ba har sai ’yan gudun hijira sun koma gidajensu
- Najeriya 66: Gwamnati ta ce sauye-sauyen tattalin arziki sun kafa tubalin ci gaba
Ya ce Najeriya na buƙatar a bai wa Afirka aƙalla kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya, tare da cikakken haƙƙi da nauyin da ke tattare da kujerar, ciki har da ikon amfani da veto.
Shettima ya kuma nemi a bai wa Afirka kujeru biyar da bana dindindin ba a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya, domin nahiyar ta samu cikakkiyar wakilci wajen yanke shawarar da suka shafi tsaron duniya.