Gwamnatin Jihar Ogun da kamfanin DP World sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin haɓaka tashar ruwa mai zurfi ta Gateway da kuma shiyyar tattalin arziki ta Blue Marine a jihar.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a Paris, da ke Faransa, inda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa masu zuba jari cewa gwamnatin tarayya za ta samar da ingantaccen tsarin dokoki da daidaiton manufofi da yanayin kasuwanci mai sauƙin hasashe domin ƙarfafa jarin cikin gida da na ƙasashen waje.

A cewar sanarwar Fadar Shugaban Ƙasa, yarjejeniyar ta ƙunshi zuba jari na farko da ya haura dala biliyan 7, yayin da ake hasashen ayyukan za su samar da guraben aiki sama da 50,000 kai tsaye, tare da ƙarin ayyukan yi a sassa daban-daban na tattalin arziki.

Shugaba Tinubu ya ce tashar ruwan da za a gina a yankin Ogun Waterside za ta kasance da tsawon wurin ɗora kaya na kilomita huɗu da zurfin mita 18, abin da zai ba ta damar karɓar manyan jiragen ruwa.

Ya ce hakan zai taimaka wajen rage cunkoso a tashoshin Apapa da Tin Can Island, tare da rage kuɗaɗe da jinkirin da masu shigo da kaya da masu fitar da kayayyaki ke fuskanta.

Gwamnatin ta kuma ce shiyyar tattalin arzikin ta Blue Marine za ta mamaye fili mai girman hekta 10,000, inda ake sa ran za a sarrafa albarkatun cikin gida da samar da kayayyakin da za a fitar da su zuwa ƙasashen waje, tare da ƙirƙirar damammakin aiki ga matasa.

Tinubu ya ce tashar ruwan za ta kasance muhimmin ginshiƙi ga shiyyar masana’antar, tare da haɗa yankin da Lagos, sauran sassan Najeriya da kasuwannin nahiyar Afirka.

Shugaban Ƙasa ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta taimaka wajen samar da hanyoyin mota da layin dogo da wutar lantarki, tare da ƙarfafa tsaron zuba jari da rage matsalolin hukumomi da ka iya kawo cikas ga aiwatar da ayyukan.

A cewarsa, ayyukan za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin teku da kuma rage dogaro da man fetur, yayin da Najeriya ke ƙoƙarin zama babbar cibiyar kasuwanci da sufuri da fitar da kayayyaki a yammacin Afirka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *