Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya amince da sabon tsarin kwamitin yaƙin neman zaɓensa gabanin babban zaɓen 2027, inda aka naɗa Sanata Augustine Okwudiri Akobundu a matsayin Darakta-Janar na Yaƙin Neman Zaɓe.
Sanarwar da Daraktan Sadarwar Dabaru na kwamitin, Phrank Shaibu, ya fitar ta ce Kashim Ibrahim-Imam ne zai jagoranci kwamitin, yayin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.
Sabon tsarin ya ƙunshi mataimakan daraktoci guda shida da kuma daraktoci 30 da za su kula da sassa daban-daban na ayyukan yaƙin neman zaɓen.
- Tinubu ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya
- Shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara ya kuɓuta daga hannun ’yan ta’adda bayan watanni biyu a tsare
Tsohon ɗan jarida kuma mawallafi, Dele Momodu, zai jagoranci sashen yaɗa labarai da sadarwa, yayin da tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, zai kasance cikin jagorancin hulɗa da jama’a da tattara goyon baya.
Sanata Akobundu, wanda ke wakiltar Abia ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, tsohon Kanal ne a rundunar sojin Najeriya kuma ya taɓa zama Ministan Ƙasa na Tsaro a gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.
Ya kuma riƙe wasu muƙamai a cikin harkokin gudanarwar jam’iyyar.
A cikin tsarin kuma akwai ƙungiyar masu ba da shawara, wadda tsohon Gwamnan Edo kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, zai jagoranta, yayin da Mohammed Hayatu-Deen zai jagoranci ɓangaren tsara manufofi tare da wasu masana da suka haɗa da Farfesa Kingsley Moghalu.
Sanarwar ta ce kafa kwamitin na nuna sabon mataki na tsari, da daidaita ayyuka da faɗaɗa shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen ADC a faɗin ƙasar gabanin zaɓen 2027.