Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ’yan takarar gwamnan jam’iyyar da mambobin kwamitin gudanarwarta na ƙasa daga jihohi 36 a Abuja.
Gombe ya ce taron na da nufin ƙarfafa shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen 2027, ta hanyar tattaunawa kan dabaru, musayar ƙwarewa da kuma daidaita ayyukan ’yan takararta.
- An ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a Ogun, an kashe wanda ake zargi
- Kotu ta yi watsi da ƙarar Maihaja, ta tabbatar da nasarar Baba Mallam Wali
Ya jaddada cewa SDP ba ta cikin wata yarjejeniya ta haɗa kai a ƙarƙashin shirin Rainbow Coalition, duk da cewa jam’iyyar za ta iya haɗin gwiwa da sauran jam’iyyun adawa domin kare dimokuraɗiyyar ƙasar.
Shugaban jam’iyyar ya yi zargin cewa ƙoƙarin kafa irin wannan ƙawance zai iya raunana jam’iyyun adawa da tsarin da suke da shi.
Ya ce SDP ta mayar da hankali ne wajen ƙarfafa matsayinta domin samun nasara a zaɓen 2027, a matakin jihohi da na ƙasa.