Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta cire bayanan masu zaɓe sama da miliyan 1.6 bayan amfani da na’urar tantance bayanan halittar jiki (ABIS) domin gano rajista iri ɗaya da sauran kura-kurai.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya ce an kuma sake tantance bayanan bayan hukumar ta bai wa jama’a damar duba rajistar wucin gadi tare da gabatar da ƙorafe-ƙorafe tsakanin 9 zuwa 15 ga Oktoba, 2026.
- ’Yan sanda sun kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Yabo
- Tinubu ya taya jakadan Najeriya a Rasha murnar cika shekara 70 da haihuwa
A cewar hukumar, an cire rajista 1,608,660 da aka tabbatar ba su inganta ba, sannan aka cire bayanan mutane 873 da aka tabbatar sun rasu.
An kuma gano wasu jami’an rajista 54 a jihohi 10 da ake zargi da hannu a kura-kuran, waɗanda za su fuskanci bincike da yiwuwar gurfanarwa.