Rundunar ta bayyana cewa an kai samamen ne da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar 8 ga Nuwamba, 2026, a ƙauyen Dan Tafki da tsaunukan da ke kusa da yankin Binji Musa.
Sanarwar da kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar a ranar 9 ga Nuwamba, ta ce jami’an rundunar ’yan sanda ta musamman mai lamba 7PMF sun haɗa kai da sashen yaƙi da manyan laifuka da na yaƙi da garkuwa da mutane wajen kai samamen.
- Wike ya yi alƙawarin sake fara aikin hanyar Kwaita-Yebu da ke Abuja
- Wike ya nemi al’ummar Abuja su goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027
Ta ce jami’an tsaron sun yi musayar wuta da ’yan bindigar na tsawon sa’o’i, kafin waɗanda ake zargin su tsere, suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su a wurin.
Waɗanda aka kuɓutar ɗin su ne Nafisa Abubakar da Aminu Sahabi, dukkaninsu mazauna ƙauyen Dono. Rundunar ta ce an garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu da ba su kulawar da ta dace.
Rundunar ta ƙara da cewa jami’an tsaron sun ƙona rumbuna da maboyar ’yan bindigar da dama.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Hayatu Hassan Shaffa, ya yaba wa jami’an bisa nasarar aikin, tare da kira ga al’umma su riƙa kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga jami’an tsaro.