Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin ba kansilan da ya tabbatar da nasarar jam’iyyar a mazaɓarsa Naira miliyan 10 domin tallafa wa gangamin zaɓen 2027.
Wike ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar Rainbow Coalition a ƙaramar hukumar Kwali ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.
- Wike ya nemi al’ummar Abuja su goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027
- Wike ya yi alƙawarin sake fara aikin hanyar Kwaita-Yebu da ke Abuja
Ya ce zai shirya gangami na musamman domin ganin an samu nasarar Shugaba Bola Tinubu da ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Ministan ya bayyana cewa kansilolin suna da muhimmiyar rawar takawa wajen kai saƙon yaƙin neman zaɓe ga al’ummar da suke wakilta.
Ya ce duk kansilan da ya yi aiki yadda ya kamata har ya tabbatar da nasarar jam’iyyar a mazaɓarsa zai samu Naira miliyan 10.