Wike ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026, yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Kwali ta Abuja.
- Sojoji sun kama dillalin makamai, sun kashe ’yan ta’adda biyu a Filato
- Bakin haure da ‘yan gudun hijira 21 sun mutu yayin da suke kokarin isa tsibirin Crete na kasar Girka
Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba na gari wanda ba ya tsoron ɗaukar matakai masu wahala domin amfanin ƙasa da al’ummarta.
Ministan ya kuma yaba wa shugabannin ƙananan hukumomi da na jam’iyyun APC da PDP a Abuja bisa haɗin kai da suke yi wajen gudanar da ayyukan ci gaba, duk da bambancin jam’iyyunsu.
Ya ce ci gaban Abuja ya fi buƙatar haɗin kan al’umma fiye da bambancin siyasa, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da wannan haɗin kai.