Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayar da umarnin korar karamin jakadan kasar Lebanon a birnin Detroit da ke jihar Michigan, Ibrahim Charara, bisa wani kalami da ake zargin ya wallafa a kafafen sada zumunta a shekarar 2021, inda ya nuna goyon baya ga kisan sojojin ruwan Amurka da aka yi a shekarar 1983.
Wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Arab News
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce an ayyana Charara a matsayin wanda ba a maraba da shi a Amurka, sakamakon sakon da ake zargin ya wallafa, inda ya bayyana harin da aka kai kan barikin sojojin ruwan Amurka da ke birnin Beirut a matsayin wani abin koyi na gwagwarmayar ‘yanci da ya kawo karshen mamayar sojojin Amurka.
- Janar Abou Issa ya karɓi ragamar shugabancin rundunonin sojin Bénin
- Mutane hudu sun mutu, wasu dari da ashirin sun jikkata sakamokon hadarin jirgin kasa a Masar
- China za ta riƙa cin tarar Yuan 100,000 ga masu yaɗa shawarwarin ƙarya a kafafen sada zumunta
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta aikewa jaridar Arab News, ta ce tana ci gaba da nazarin bayanan jami’an kasashen ketare da ke da izinin gudanar da ayyukansu a Amurka, ciki har da duk wata barazana ga tsaron kasa, tare da daukar matakan da suka dace bisa dokokin Amurka da yarjejeniyoyin kasa da kasa.
Ma’aikatar ta kara da cewa ‘yan ta’adda sun kashe Amurkawa da abokan aikinsu a hare-haren bam da aka kai kan ofisoshin jakadancin Amurka da ke Beirut a shekarun 1983 da 1984, tana mai cewa ba za ta taba mantawa da wadanda suka rasa rayukansu ba.
Ta kuma jaddada cewa an ayyana karamin jakadan Lebanon da ke Detroit a matsayin wanda ba a maraba da shi a Amurka, tana mai cewa samun bizar shiga kasar gata ne, ba wani hakki ba.
Sanarwar ta kara da cewa duk wanda ke Amurka yake murna ko kuma ba da hujjar hare-haren ta’addanci, bai cancanci zama a kasar ba.
An danganta sakon da shafin Twitter na Charara a lokacin da yake rike da mukamin ministan harkokin wajen Lebanon a kasar Masar a shekarar 2021, ta amfani da sunan mai amfani da shafin @IbrahimChararaa. Sai dai shafin ya daina aiki tun watan Nuwamban 2021.
Harin bam da aka kai kan barikin sojojin Amurka a Beirut a ranar 23 ga Oktoban 1983, wanda ake dangantawa da kungiyar Hezbollah, ya faru ne a lokacin yakin basasar Lebanon.
A yayin harin, wasu ‘yan kunar bakin wake sun tuka manyan motoci dauke da bama-bamai zuwa sansanonin da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashe daban-daban ke amfani da su a Beirut.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an sojin Amurka 241, ciki har da sojojin ruwa 220, tare da jikkata wasu sama da 100.
An nada Charara a matsayin karamin jakadan Lebanon a ranar 25 ga Satumban 2025. Kafin wannan mukami, ya yi aiki a ma’aikatar harkokin wajen Lebanon da kula da ‘yan kasarta da ke kasashen waje tun watan Yunin 2016.