Mutane akalla hudu ne suka mutu, yayin da wasu 88 suka jikkata sakamakon karo da jiragen kasa biyu suka yi a kudancin birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, a ranar Lahadi.
Hukumomin kasar sun ce hadarin ya yi sanadiyyar karkacewar taragon da ke jigilar fasinjoji daga kan layin dogo.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Masar ta bayyana cewa wani jirgin kasa da ke tafiya daga Giza zuwa Fayoum ya fadi bayan wani jirgin da ke kan hanyarsa daga Alkahira zuwa birnin Aswan da ke kudancin kasar a samu matsala.
- Trump ya ce Amurka a shirye take ta sake ɗaukar manyan matakai a binciken sararin samaniya
- Najeriya da Turkiyya za su ƙarfafa haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai da yaƙi da yaɗa labaran ƙarya
- Najeriya ta nemi UN ta kammala ayyukanta cikin kasafin kudi da wa’adin da aka shata
Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta ce rahoton farko ya nuna cewa fasinjoji hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 88 ke samun kulawar likitoci a asibitocin yankin Giza sakamakon raunukan da suka samu.
Tun da farko Kafofin yada labaran kasar mallakar gwamnati sun ruwaito cewa mutane 120 ne suka jikkata, sai dai ba su bayyana irin raunukan da suka samu ba.
Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya ce yana bibiyar lamarin cikin matukar damuwa, inda ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike cikin gaggawa domin hukunta duk wanda aka samu da sakaci.
Hukumar kula da jiragen kasan ta ce jami’an agaji sun yi amfani da manyan na’urorin wajen cire tarkacen jiragen da suka yi hadarin.
A shekarar 2002, sama da mutane 370 ne suka mutu bayan wata gobara ta tashi a cikin wani jirgin kasa da ke dauke da matafiya zuwa kudancin Alkahira.
Haka kuma, a shekarar 2009, wasu hadurran jiragen kasa da dama da suka faru a yankin sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Kasar Masar mai yawan al’umma kusan miliyan 110, ta dogara matuka da sufurin jiragen kasa wajen zirga-zirgar jama’a, sai dai hanyar jiragen kasarta, wadda ke cikin manyan hanyoyin jiragen kasa a Afirka, ta sha fuskantar hadurra masu jawo asarar rayuka.
A cikin shekaru goma da suka gabata, gwamnatin Masar ta kashe biliyoyin daloli wajen inganta ababen more rayuwa na sufuri, ciki har da gina sabbin manyan tituna da layukan dogo na jiragen kasa masu saurin gaske.
Sai dai har yanzu ba a yi cikakken gyara da zamanantar da mafi yawan tsofaffin layukan dogo na kasar ba.