Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kama wani matashi mai shekara 20 bisa zargin taimaka wa ’yan bindiga a ƙauyen Tafkin Kaiwa da ke Ƙaramar Hukumar Dange-Shuni a Jihar Sakkwato.
Rundunar ta ce an kama matashin ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri.
- ADC ta ce Tinubu zai sha kaye a zaɓen 2027
- Kamfanin siminti na Dangote ya tallafa wa ’yan kasuwa 15 a Kogi
A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa yana taimaka wa ’yan bindiga, ciki har da gayyatar wani fitaccen shugaban ’yan bindiga daga Jihar Zamfara domin kai hari ƙauyensa da satar shanu a watan Satumba.
A cewar rundunar, wanda ake zargin na bayar da bayanai masu amfani ga masu bincike domin gano sauran mutanen da ke cikin ƙungiyar.
Rundunar ’yan sandan ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin domin gano cikakken tsarin hulɗar da ake zargin yana tsakaninsa da ’yan bindigar.