Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, duk da abin da ta kira barazana, tashin hankali da amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa wa ’yan adawa.

Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya zargi gwamnatin APC da yin katsalandan a harkokin shari’a da amfani da jami’an tsaro wajen tsoratar da ’yan adawa.

Ya yi zargin cewa wasu ’yan daba masu goyon bayan APC sun kai hari kan wurin taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar NDC a Jihar Delta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu mambobinta.

Ya kuma ce ana kai hare-hare kan ’yan ADC, NDC da APM a wasu jihohi.

ADC ta kuma yi zargin cewa an yi wa kundin rajistar masu zaɓe na INEC katsalandan, tare da tura magoya bayan APC zuwa muhimman muƙamai a hukumar.

Ta kuma zargi jami’an tsaro da amfani da ikonsu wajen tsarewa da tsoratar da ’yan adawa.

Jam’iyyar ta buƙaci ’yan Najeriya su kare ƙuri’unsu da ’yancinsu na dimokuraɗiyya, sannan ta yi kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin fararen hula su sanya ido kan yanayin siyasar ƙasar gabanin zaɓen 2027.

Ta kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kasance masu bin kundin tsarin mulki, ba tare da nuna goyon baya ga wata jam’iyya ba, tana mai jaddada cewa barazana ko amfani da hukumomin gwamnati ba za su hana ’yan Najeriya zaɓen wanda suke so ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *