Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wata ’yar ƙasar Uganda mai shekara 34, da ƙunshin hodar iblis 87 masu nauyin kilogram 1.15, waɗanda ta ɓoye a sassan al’aurarta domin fitar da su zuwa ƙasarta.

Hukumar ta ce an kama matar ne a ranar 3 ga Nuwamba, 2026, a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, lokacin da take shirin shiga jirgin da zai mayar da ita Uganda.

A yayin bincike, jami’an NDLEA sun gano ƙunshin ƙwayoyin da aka ɗaure a gefen ƙugu, a ƙarƙashin riguna biyu.

Matar ta ce ta zo Najeriya ne tare da wasu ’yan cocinta domin halartar taron addu’a a Cocin Synagogue da ke Ikotun, Legas, amma ta tsaya bayan sauran tawagarta sun koma Uganda domin karɓar kayan da wani abokinta ya turo mata.

A wani samame kuma, hukumar ta kama ƙwayoyin Tapentadol 750,000 masu darajar Naira miliyan 900 a filin jirgin saman Legas wadan da aka shigo da su daga Indiya a cikin kwali 11.

NDLEA ta kuma kama miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi, Tramadol da sinadarai da ake amfani da su wajen ƙera tabar wiwi ta roba a Legas da wasu jihohi.

A Jihar Ondo kaɗai, jami’an hukumar sun kwato buhuna 148 na tabar wiwi masu nauyin kilogram 1,818, tare da lalata gonar tabar wiwi mai girman hekta ɗaya.

Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen, yana mai cewa lamarin matar Uganda ya nuna yadda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da tafiye-tafiyen addini wajen yaudarar mutane da ɗaukar su aikin safarar ƙwayoyi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *