Tsibirin dai ya kasance daya daga cikin muhimman wuraren da ‘yan gudun hijira da masu kaura ke bi domin shiga nahiyar Turai, kamar yadda hukumomi kasar Girka suka bayyana.
Jami’an tsaron gabar tekun kasar sun ce sun gano gawarwakin mutane 12 tare da ceto wasu mutane 18 daga cikin wani jirgin ruwa da wani babban jirgin dakon kaya mai tutar kasar Morocco ya hango a kudancin tsibirin da safiyar ranar Litinin.
Sun ce sun kai wadanda suka tsira da kuma gawarwakin mutanen zuwa gabar teku. Sai dai daga cikin wadanda aka ceto, wani mutum da aka kai asibiti ya rasu daga baya.
- Janar Abou Issa ya karɓi ragamar shugabancin rundunonin sojin Bénin
- Mutane hudu sun mutu, wasu dari da ashirin sun jikkata sakamokon hadarin jirgin kasa a Masar
- China za ta riƙa cin tarar Yuan 100,000 ga masu yaɗa shawarwarin ƙarya a kafafen sada zumunta
Ba a bayyana musabbabin mutuwar mutanen nan take ba, amma hukumomin Girka sun ce akwai yiwuwar jirgin ya shafe kwanaki a cikin teku, yana fama da wahalar isa gabar teku sakamakon karfin iska.
A wani lamari na daban, jami’an tsaron gabar teku na Girka sun gano gawarwakin mutane takwas tare da ceto wasu ‘yan gudun hijira da masu kaura 28 daga wani jirgin ruwa a kudancin tsibirin Crete a yammacin ranar Asabar.
Haka kuma, har yanzu ba a gano wasu mutane biyu da suka bace ba.
An kuma gano wasu jiragen ruwa biyu a kudancin tsibirin Crete, dake dauke da mutane kusan 47, yayin da dayan kuma ke dauke da mutane kusan 40.
Hukumar kula da iyakokin Tarayyar Turai (Frontex) ta yi amfani da jirgin sama da kuma wani jirgi marar matuki wajen gano jiragen ruwan, kafin daga bisani ta taimaka wajen kai wadanda suka tsira zuwa wani tashar jiragen ruwa da ke kudancin tsibirin Crete.
Tsibirin Crete ya zama daya daga cikin manyan hanyoyin shiga Tarayyar Turai ga mutanen da ke tserewa daga rikice-rikice da talauci a yankin Gabas ta Tsakiya, Afirka da Asiya.
Hukumar Hukumar Kula da Iyakokin Tarayyar Turai Frontex ta ce yawan mutanen da ke tsallakawa zuwa Tarayyar Turai ta hanyoyin da ba bisa ka’ida ba ya ragu da kashi daya bisa uku a bana.
Hukumar ta bayyana cewa an samu kusan mutane 31,800 da suka shiga Tarayyar Turai ta irin wadannan hanyoyi a cikin watanni tara na farkon shekarar 2026, adadin da ya nuna raguwar kashi 15 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.