Dakarun Sojojin Najeriya sun kama wani mutum da ake zargin dillalin makamai ne, sun kashe ’yan ta’adda biyu tare da rusa sansanoninsu a wasu samamen tsaro da suka kai a ƙananan hukumomin Mangu, Kanam da Wase na Jihar Filato.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce jami’an rundunar tabbatar da zaman lafiya ta Operation Enduring Peace sun kama wanda ake zargin, a kasuwar Gindiri da ke ƙaramar hukumar Mangu, bisa bayanan sirri.
An kama shi ne tare da bindigar AK-47 guda ɗaya da alburusai 15 masu girman 7.62mm, kuma a halin yanzu yana hannun jami’an tsaro domin gudanar da bincike.
- Yadda ’yan bindiga suka ƙona mutum 12 ‘yan gida ɗaya bayan sun ƙi buɗe musu ƙofa a Zamfara
- ’Yan sanda sun ceto shugaban APC na Rogo bayan shafe kwanaki 68 a hannun masu garkuwa
A wani samamen kuma, dakarun runduna ta 33 sun kai farmaki a dajin Dajin Madam, wanda ya ratsa ƙananan hukumomin Kanam da Wase, inda suka rusa sansanonin ’yan ta’adda tare da lalata wuraren da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Sanarwar ta ce dakarun sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan, inda suka tilasta musu ja da baya. Daga bisani, sun ƙwato alburusai 135, wayoyin hannu huɗu, rediyoyi biyu, babura huɗu, gangunan man fetur guda biyu, kayan soji da wasu kayayyakin sadarwa.
A wani artabu kusa da ƙauyen Kukawa kuma, sojojin sun kashe ’yan ta’adda biyu tare da ƙwato wasu babura.
Rundunar sojin ta ce za ta ci gaba da kai samame domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka, tare da ƙwace makamansu da kayayyakin da suke amfani da su, don dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.