Wike ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Kwali ta Abuja a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.
- Wike ya nemi al’ummar Abuja su goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027
- Bakin haure da ‘yan gudun hijira 21 sun mutu yayin da suke kokarin isa tsibirin Crete na kasar Girka
Ya ce an samu tsaiko a aikin ne saboda rashin ƙarfin kamfanin da aka bai wa kwangilar, lamarin da ya sa aka soke kwangilar.
Ministan ya ce zai bai wa wani kamfani mai ƙarfin gudanar da aikin kwangilar domin tabbatar da kammala hanyar.
Ya kuma yi alƙawarin shiga tsakani domin ganin an magance matsalolin da suka shafi gadar Ebbo da ta haɗa ƙananan hukumomin Abaji da Kuje.