Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya nuna damuwa kan ƙarancin wakilcin mata a majalisun kansilolin ƙananan hukumomin babban birnin tarayya.
Wike ya bayyana cewa daga cikin kujerun kansiloli 62 da ake da su a Abuja, mata biyu ne kawai suka samu wakilci.
- Wike ya nemi al’ummar Abuja su goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027
- ’Yan sanda sun kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Yabo
Ya yi wannan jawabi ne yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Kwali ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.
Ministan ya buƙaci a ƙara yawan matan da za su samu damar shiga harkokin shugabanci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da wakilci ga kowa.
Ya ce ba ya nufin a hana maza damar samun mukamai, sai dai mata da ’ya’ya mata su ma su samu damar taka rawa a tsarin mulki.