Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake yin kira da a sauya tsarin Majalisar Dinkin Duniya, musamman Kwamitin Tsaro, domin Afirka ta samu wakilcin dindindin da cikakken ikon da ya rataya a kan wannan matsayi.
A jawabin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gabatar a madadin Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 da ke gudana a New York, shugaban ya ce bai dace duniyar 2026 ta ci gaba da tafiya da tsarin rabon iko da aka kafa tun 1945 ba.
Tinubu ya nemi Afirka ta samu aƙalla kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaro, tare da kujeru biyar wadan da bana dindindin ba.
- Wike ya ce hanyar Apo-Karshi da Bwari-Kubwa za su kammala nan da Disamba
- Kotu ta soke tikitin Pantami, ta umarci PDP ta sake zaɓen fidda gwani a Gombe.
Ya kuma ce idan har aka ci gaba da riƙe ikon amfani da veto, ya kamata sabbin kujerun dindindin na Afirka su samu irin wannan dama.
Wannan matsaya ya yi daidai da matsayin Afirka da aka bayyana a yarjejeniyar Ezulwini Consensus da Sirte Declaration.
Shugaban ya kuma yi kira da a kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a duniya cikin gaggawa, tare da komawa ga tattaunawa, da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
Tinubu ya ce Najeriya za ta ci gaba da taka rawa wajen samar da zaman lafiya a Afirka, yana mai tunatar da irin gudunmawar da ƙasar ta bayar a Liberia, da Saliyo, da Darfur, Mali da Gambia, tare da ayyukan ECOWAS da Tarayyar Afirka wajen magance matsalolin tsaro.
A fannin tattalin arziki, shugaban ya nemi a sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya domin ƙasashe masu tasowa su samu sauƙin samun kuɗin raya ƙasa da kuma tsarin biyan basussuka da zai yi la’akari da buƙatun ci gaba.
Ya kuma yi kira da a yi wa Afirka adalci wajen tallafin kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, yana mai cewa nahiyar na fuskantar mummunan tasirin sauyin yanayi duk da cewa gudunmawarta ga hayakin da ke ɗumamar duniya bai kai kashi huɗu cikin ɗari ba.
Najeriya ta sake tabbatar da aniyarta kan Yarjejeniyar Paris da kuma sauyin makamashi cikin adalci.