Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce gwamnatinsa ba za ta sassauta wajen yaƙi da ’yan bindiga ba har sai an samar da isasshen tsaro da zai bai wa mutanen da suka rasa matsugunansu damar komawa gidajensu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin buɗe taron Majalisar Zartarwar Jihar Sokoto karo na takwas, inda ya ce haɗin gwiwar gwamnati da jami’an tsaro na samar da sakamako mai kyau wajen yaƙi da ’yan bindiga.
Ya ce ana samun ci gaba a wasu yankunan jihar, inda jami’an tsaro suka kuɓutar da wasu mutane daga hannun ’yan bindiga tare da kwato dubban dabbobin da aka sace a Rabah, da Tureta da Kebbe.
- Najeriya da DP World za su zuba sama da dala biliyan 7 a tashar ruwa da ke Ogun
- Atiku ya naɗa Akobundu shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, El-Rufai ya zama mataimakinsa
Gwamnan ya ce gwamnati za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro tallafi, ciki har da sabbin motocin sulke da sauran kayan aiki, domin ba su damar ci gaba da bibiyar ’yan bindiga tare da kare al’ummomin karkara.
Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da bai wa gwamnati da jami’an tsaro haɗin kai domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa, musamman a yankunan da hare-haren ’yan bindiga suka fi shafa.
A cewar Gwamna Aliyu, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a, musamman a fannonin lafiya da ilimi da hanyoyi da samar da ruwa da shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki.