Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta ce ta kama mutum biyu da ake zargi da hannu a kashe mutane biyu a wasu sassan jihar, ciki har da wata jaririya mai watanni huɗu.

A Zirami da ke yankin Azare, an kama wani matashi mai shekaru 27 bayan an samu gawar ’yarsa, mai watanni huɗu.

Mahaifiyar jaririyar ta ce ta bar ta tana barci, amma bayan ta dawo ta same ta ba ta numfashi, sannan ta ga mijinta yana fitowa daga ɗakin.

Binciken likita ya tabbatar da cewa jaririyar ta mutu ne sakamakon shake ta.

A wani lamari kuma a ƙauyen Wasari da ke Gadau, an kama wani mai shekaru 25 bisa zargin kashe wata mata mai shekaru 60.

’Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya shiga gidan matar ne, ya yanka mata wuya tare da daba mata wuka, yana zargin ta da tsafi da haddasa rashin lafiyar wata ’yar unguwarsu.

Rundunar ’yan sandan Bauchi ta ce duka shari’o’in suna karkashin bincike, kuma za a mika su zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin zurfafa bincike.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da kisan da ya shafi zargin tsafi da kuma cin zarafin mata da yara, tare da gargadin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *