Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya caccaki wakilan ƙasashe da suka fice daga zauren Majalisar Ɗinkin Duniya yayin da ya fara jawabinsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da ke New York.

Yayin da wakilan ƙasashe da dama ke barin zauren, Netanyahu ya mayar da martani cikin kalamai masu zafi, inda ya kira waɗanda suka fita da “matsoratan ɗabi’a”, tare da cewa sauran waɗanda ke shirin fita su ma su bi sahunsu.

Netanyahu ya ce Isra’ila ba za ta ja da baya wajen kare kanta ba, yana mai kare matakan sojin ƙasar kan Iran da Hamas.

Ya kuma yi ikirarin cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran sun kasance matakin da ya zama dole domin kare Isra’ila da sauran ƙasashe.

Dangane da yakin Gaza, Netanyahu ya yi watsi da zarge-zargen cewa Isra’ila na aikata kisan kare dangi, inda ya kira irin waɗannan zarge-zarge “babbar ƙaryar ƙarni”.

Ya kuma zargi Hamas da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa, tare da kare matakan da Isra’ila ta ce tana ɗauka domin kare fararen hula.

Jawabin Netanyahu ya zo ne a daidai lokacin da Isra’ila ke fuskantar suka daga wasu shugabannin duniya kan yakin Gaza.

Ficewar wakilan daga zauren yayin da ya fara magana ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a zaman Majalisar Ɗinkin Duniyar na bana.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *