Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, ya musanta ikirarin cewa ya bar jihar da bashin dala miliyan 123.77, yana mai cewa kudaden da ake magana a kai sun haɗa da shirye-shiryen tallafin raya ƙasa da gwamnatin tarayya ta samo daga Bankin Duniya da IFAD.

Obi ya ce a lokacin da yake gwamna bai nemi rance daga wata cibiyar kuɗi ba, kuma bai fitar da bond a madadin gwamnatin Anambra ba.

Ya ce bai dace a haɗa jimillar kudaden da aka amince da su da waɗanda aka raba ko aka janye a zahiri a kira su duka bashin da ya bari ba.

Ya kuma ce bayanan Hukumar Kula da Basussukan Najeriya, DMO, sun nuna cewa bashin waje na Anambra ya kai kusan dala miliyan 18 a lokacin da ya karɓi mulki a 2006, sannan kusan dala miliyan 30 lokacin da ya bar mulki a Maris 2014.

Sai dai gwamnatin Anambra ta ce akwai rance na waje guda takwas da aka kulla a lokacin mulkin Obi, wanda jimillarsa ta kai dala miliyan 123.77, yayin da kusan dala miliyan 92.35 ke kan gaba a matsayin ragowar bashi zuwa Yuni 2026.

Gwamnatin ta ce tana ci gaba da biyan bashin.

Obi ya kuma ce ya bar sama da dala miliyan 150 a matsayin kudade da jarin da ya kamata su samar wa jihar kuɗin shiga, yana mai cewa takardun da ke tabbatar da hakan za a iya tantance su.

Ya ce ba ya son ci gaba da musayar kalamai da gwamnatin Anambra kan batun, yana mai cewa hankalinsa zai koma kan matsalolin da ke addabar al’ummar Najeriya da kuma burinsa na neman shugabancin ƙasa a 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *