An gurfanar da wasu mutane biyar a gaban kotu a Maiduguri, Jihar Borno, bisa zargin sanya riguna masu ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”, wato “Tinubu dole ya tafi”.

Mutanen sun haɗa da mai shekara 44, da mai shekara 28, da mai shekara 32, da mai shekara 21 da mai shekara 21.

Rahotanni sun ce an kama su ne a ranar 25 ga Satumba, 2026, a yankin West End Roundabout da ke Maiduguri, bayan jami’an tsaro sun gan su sanye da rigunan da ke ɗauke da taken.

A cewar takardar tuhumar ‘yan sanda, ana zargin mutanen da haɗa baki, da tayar da tarzoma, da kawo cikas ga zaman lafiya da kuma daba.

‘Yan sandan sun kuma yi zargin cewa an shirya rigunan ne da nufin haifar da tashin hankali.

An gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Majistare ta ɗaya da ke Maiduguri, inda mutanen biyar suka musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

Lauyoyinsu sun nemi kotun ta bayar da belinsu, amma an dage sauraron buƙatar belin zuwa ranar 6 ga Oktoba, 2026. Haka kuma, an sanya ranar 26 ga Oktoba domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Rahotanni sun ce an ci gaba da tsare mutanen yayin da ake jiran sauraron buƙatar belin, sai dai wasu kungiyoyi da ‘yan siyasa sun soki kamen, suna cewa bayyana ra’ayin siyasa cikin lumana na daga cikin ‘yancin ɗan ƙasa.

Kungiyar Amnesty International ta kuma yi kira ga hukumomi da su saki mutanen, yayin da wasu masu fafutukar siyasa suka bukaci a tabbatar da cewa ana mutunta ‘yancin faɗar albarkacin baki.

Sai dai zarge-zargen da ake yi wa mutanen biyar ba su zama hukunci ba, domin har yanzu shari’ar tana gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *