A shekarar 1960, sadarwa a Najeriya ta kasance abu ne da ya fi karkata ga wayoyin ofis, da gidan waya da sauran hanyoyin sadarwa na gargajiya.

Yau kuma, wayar hannu ta zama kayan aiki na yau da kullum, intanet na taimakawa kasuwanci da ilimi, yayin da fasahar ƙera bayanai da basirar wucin gadi ke fara sauya yadda ake aiki da gudanar da harkokin gwamnati.

Wannan canjin ya yi matuƙar sauri musamman tun bayan bunƙasar harkar sadarwar zamani.

Bayan shekaru da dama da ake fama da ƙarancin damar sadarwa, Najeriya a yanzu tana da sama da masu biyan kuɗin intanet na broadband miliyan 124.4, bisa bayanan Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, na Yuli 2026. Wannan adadi ya nuna girman yadda damar amfani da intanet ta yaɗu idan aka kwatanta da shekarun baya.

Haka kuma, bayanan NITDA sun nuna girman sauyin da aka samu a fannin.

Hukumar ta ce lokacin da aka kafa ta a 2001, ƙasar da ’yan Najeriya 500,000 ne ke da damar amfani da kwamfuta, yayin da fannin ICT ke bayar da kashi 0.05 cikin 100 na GDP.

A yanzu kuma, NITDA ta ce sama da ’yan Najeriya miliyan 130 suna amfani da intanet, yayin da ICT ke bayar da fiye da kashi 17 cikin 100 na GDP.

Sai dai akwai bambanci tsakanin yawan layukan intanet da yawan mutanen da ke amfani da intanet, don haka alkaluman NCC da NITDA ba lallai ne su kasance ma’auni iri ɗaya ba.

Abin da suke tabbatarwa shi ne cewa Najeriya ta samu gagarumin faɗaɗa damar sadarwa, duk da cewa ingancin sabis da daidaiton samun damar amfani da intanet tsakanin birane da karkara har yanzu na daga cikin manyan ƙalubale.

NCC ta ce rahotannin aikin cibiyoyin sadarwa na 2026 suna ci gaba da nuna bambance-bambancen inganci tsakanin yankuna.

A wannan sabon zamani, gwamnati ma ta fara kallon intanet da bayanai a matsayin muhimmin ɓangare na ababen more rayuwa.

A watan Agustan 2026, Ma’aikatar Sadarwa, da Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Dijital ta ƙaddamar da National Digital Cloud Policy, wadda ke neman jawo jarin kamfanoni wajen gina cibiyoyin adana bayanai da cloud, da inganta ayyukan gwamnati na zamani da kuma mayar da Najeriya cibiyar ayyukan dijital a Afirka.

Gwamnati ta kuma ce tana son tara aƙalla dala miliyan 250 na jarin kamfanoni a cikin watanni 12 na farko.

A fannin samar da ƙwararrun ma’aikata kuma, Project BRIDGE na gwamnatin tarayya na da shirin gina kusan kilomita 90,000 na hanyar fiber-optic domin faɗaɗa haɗin intanet a ƙasar.

An kuma tsara bincike na ƙasa kan tasirin fasahar dijital a fannoni kamar harkokin kuɗi, da ayyukan gwamnati, da kasuwancin intanet, da sadarwa da kiwon lafiya.

Sai kuma sabon babin da aka buɗe na AI wato basirar wucin gadi ta AI.

A shekarar 2026, Najeriya ta ƙara mai da hankali kan ƙirƙirar fasahar AI da ta dace da yanayin ƙasar. Misali, N-ATLAS, wani samfurin AI, an tsara shi domin fahimtar harsunan Hausa, Yarbanci, Igbo da Ingilishi mai lafazin Najeriya, tare da fasahar gane magana.

Hakan na iya buɗe damar amfani da AI wajen ilimi, lafiya, noma, harkokin shari’a da ayyukan kuɗi.

Amma kamar sauran fannoni, akwai tambayoyin da har yanzu ke bukatar amsa. Shin intanet mai sauri zai isa ga mutanen karkara da masu ƙaramin ƙarfi? Shin matasa za su samu ƙwarewar da za ta ba su damar cin moriyar tattalin arzikin dijital? Kuma ta yaya Najeriya za ta kare bayanan jama’a, DA yaƙi yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma tabbatar da cewa AI ba ta ƙara faɗaɗa gibin da ke tsakanin waɗanda ke da fasaha da waɗanda ba su da ita?

Shekaru 66 bayan samun ’yancin kai, Najeriya ta yi nisa daga zamanin da sadarwa ke tafiya a hankali zuwa lokacin da mutum zai iya aika saƙo, gudanar da kasuwanci, koyon sana’a ko amfani da AI daga wayarsa. Amma babban mataki na gaba ba wai kawai samun ƙarin mutane a intanet ba ne; shi ne tabbatar da cewa fasahar dijital ta zama hanyar samar da ilimi, ayyukan yi, ƙirƙire-ƙirƙire da damar tattalin arziki ga kowane sashe na Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *