Ministar Harkokin Yawon Buɗe Ido, Fasaha, Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musa Musawa, ta bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wani hoto da ta zana da kanta, wanda ke ɗauke da hotonsa tare da marigayiyar mahaifiyarsa.
Musawa ta bayyana hakan ne bayan ta kai wa Shugaban Ƙasa ziyarar girmamawa bayan dawowarsa Najeriya da kuma kammala bikin ƙaddamar da shirin fim ɗin MKO, wanda aka shirya domin tunawa da marigayi MKO Abiola.
- SERAP ta bukaci a yi bincike kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan 94.4 na man fetur
- Wike ya caccaki Amaechi kan maganar rasuwar mahaifiyarsa
Ministar ta ce duk da cewa zane wani abin sha’awa ne da take yi a lokacin hutunta, wannan hoton ya kasance na musamman a gare ta saboda yana ɗauke da ma’ana ta musamman game da alaƙar uwa da ɗanta.
Ta ce ta samu ƙarin ƙwarin gwiwar yin hoton ne saboda irin goyon bayan da Shugaba Tinubu ya nuna mata lokacin da ta rasa mahaifiyarta.
A watan Yunin 2026, Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga Musawa bayan rasuwar mahaifiyarta, Hajiya Fatima Musa Musawa, inda ya bayyana rasuwar uwa a matsayin babban rashi.
Musawa ta kuma nuna godiya ga Shugaban Ƙasa kan goyon baya da alherin da ta ce ya ci gaba da nuna mata, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara ba shi hikima, ƙarfi da shiriya wajen jagorantar Najeriya.