Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, NAF, ta tabbatar da mutuwar mutane 25 da ke cikin jirgin sama mai lamba NAF 931, wanda ya yi hatsari a yankin Igbokoda da ke Jihar Ondo.
A cewar rundunar, jirgin samfurin ATR 42 yana dauke da mutane 25, wadanda suka hada da ma’aikatan jirgin biyar da fasinjoji 20.
Rundunar ta kuma fitar da sunayen ma’aikatan jirgin da fasinjojin da ke cikin NAF 931, inda ta ce Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayan rundunar a wannan lokaci na bakin ciki.
- IGP Disu ya gana da babban sakataren INTERPOL a Faransa
- NEMA ta tura tawagar fasaha wurin hatsarin jirgin NAF a Ondo
NAF ta ce an umurci a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin, tare da gargadin jama’a da su guji yada jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba.
An kuma bude littafin ta’aziyya a hedikwatar rundunar da ke Abuja domin jami’an gwamnati da sauran masu son mika sakon jaje.
Hatsarin ya faru ne bayan da aka tabbatar da cewa jirgin ya yi hatsari a yankin Igbokoda, yayin da yake kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas. A baya, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa mutane 32 ne gaba daya ke cikin jirgin, wato ma’aikatan jirgin bakwai da fasinjoji 25.