Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen  ’yan takarar kujerar gwamnan Jihar Gombe na ƙarshe a zaɓen ranar 6 ga Fabrairu, 2027, ba tare da sunan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ba.

Jerin sunayen, wanda hukumar ta fitar bisa alkawarin da shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, ya yi a wani taron manema labarai a Abuja, ya ƙunshi ’yan takara 16 da aka tantance domin shiga zaɓen.

Daga cikin waɗanda sunayensu suka bayyana akwai Bala Bello Tinka na jam’iyyar ADC, Jamilu Isyaku Gwamna na APC da Babayo Ardo Kumo na NDC.

Sauran sun haɗa da Zubairu Mu’azu Halilu na Labour Party, Lamela L. Silas na APM, Ibrahim Jalo Abubakar na PRP da Adamu Mohammed Ma’aji na SDP.

Sai dai sunan Pantami, wanda ya bayyana a jerin wucin gadi da hukumar ta fitar a ranar 29 ga Agusta, bai bayyana a sabon jerin na ƙarshe ba.

Pantami ya zama ɗan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar PDP bayan ficewarsa daga APC a ranar 19 ga Mayu. Amma Ahmed Mailantarki Mailantarki, ɗaya daga cikin masu neman tikitin jam’iyyar, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar nasarar Pantami a zaɓen fidda gwani.

Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fidda gwanin tare da umartar PDP ta sake gudanar da sabon zaɓe, inda Pantami ya sake samun nasara.

Sai dai hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba ya ƙara jefa shakku kan takararsa.

Kotun ta dawo da sassan 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, waɗanda ke hana jam’iyyu tsayar da ’yan takarar da sunayensu ba su cikin rajistar mambobin jam’iyyar da aka miƙa wa INEC cikin lokacin da doka ta tanada.

A yayin da ake ci gaba da rashin tabbas kan ko Pantami zai shiga zaɓen, Kwamishinan INEC na Ƙasa, Mohammed Haruna, ya yi nuni da cewa bisa hukuncin Kotun Ƙoli, akwai jam’iyyun siyasa da ba za su iya tsayar da ’yan takara a zaɓen 2027 ba.

Haruna ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust TV.

Duk da haka, rashin sunan Pantami a jerin ƙarshe na INEC ya jawo hankalin jama’a, yayin da ake jiran ƙarin bayani kan matsayin takararsa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *