Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi maraba da sabon rahoton Bankin Duniya kan tattalin arzikin ƙasar, inda ya ce rahoton ya tabbatar da cewa gyare-gyaren da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako.

Sai dai ya amince cewa akwai sauran aiki kafin nasarorin da aka samu su inganta rayuwar al’ummar ƙasar kai tsaye.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, shugaban ya ce rahoton Bankin Duniya na watan Oktoban 2026, mai taken Bayan Kasafin Kuɗin Gwamnatin Tarayya: Yadda Ƙarin Kuɗaɗen Shiga Suka Sauya Manufofin Jihohi, ya tabbatar da cewa cire tallafin man fetur, haɗa kasuwar canjin kuɗaɗen waje da kuma tsaurara bin ƙa’idojin kashe kuɗin gwamnati sun fara daidaita tattalin arzikin ƙasar.

Tinubu ya ce, “Wannan rahoto ya tabbatar da cewa matakai masu wahala amma wajibi da muka ɗauka na cire tallafin man fetur, haɗa kasuwar canjin kuɗaɗen waje da ƙarfafa bin ƙa’idojin kashe kuɗi sun ƙara kuɗaɗen shiga, sun daidaita tattalin arziki, tare da samar wa dukkan matakan gwamnati damar zuba jari wajen inganta rayuwar al’ummarsu.”

Bankin Duniya ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a farkon rabin shekarar 2026, idan aka kwatanta da kashi 3.9 cikin 100 a makamancin lokacin shekarar 2025, duk da matsin tattalin arziki da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa.

Bankin ya kuma yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da kashi 4.4 cikin 100 ko fiye tsakanin shekarun 2026 zuwa 2028.

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu sosai daga kashi 27.6 cikin 100 a watan Janairun 2025 zuwa kashi 15.2 cikin 100 a watan Disamban shekarar.

Sai dai tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya ya rage saurin raguwar hauhawar farashin kayayyakin.

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa hauhawar farashin kayayyaki za ta ragu zuwa kusan kashi 12 cikin 100 nan da shekarar 2028.

Rahoton ya kuma gano cewa yawan talauci a Najeriya ya tsaya cak a karon farko tun shekarar 2019, tare da hasashen cewa zai fara raguwa a hankali idan tattalin arzikin ƙasar ya ci gaba da bunƙasa fiye da ƙaruwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *