Rundunar Sojin Sama ta Operation Hadin Kai ta ce ta hallaka ’yan ta’addar ƙungiyar ISWAP sama da 40, ciki har da wani babban kwamandansu, a wani harin sama da ta kai kan maboyarsu a Jihar Borno.
Sanarwar da jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar 12 ga Oktoba, 2026, ta ce harin ya faru ne a ranar 10 ga Oktoba a ƙauyen Badu, kudancin Gudumbali, cikin ƙaramar hukumar Guzamala ta jihar.
Rundunar ta ce ta gudanar da harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan ta’addar na shirin kai hare-hare kan sojojin da ke aiki a yankin da ke ƙarƙashin Sashe na Uku na rundunar.
- Atiku ya bukaci a ceto Ahmed Zakka, matarsa da jaririnsu da aka sace a Kaduna
- SERAP ta maka CBN a kotu kan zargin kashe sama da Naira tiriliyan 1.63
Bayan sa ido ta sama da gano motsin ’yan ta’addar a kusa da maboyoyinsu da wuraren ajiyar kayayyakin aiki, rundunar ta kai hari kan wani gini da suke ciki.
Binciken farko bayan harin ya nuna cewa an hallaka sama da ’yan ta’adda 40, sannan an lalata motoci biyu da babura kusan 20 da suke amfani da su wajen zirga-zirga, da jigilar kayayyaki da kai hare-hare.
Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan ta’addar na cikin ɓangaren Murabitun na ISWAP, wata runduna ta musamman da ke gudanar da sintiri, tsara hare-hare da kuma tallafa wa ayyukan ƙungiyar a yankin tafkin Chadi.
Rundunar ta ce har yanzu ana ci gaba da tantance cikakken sakamakon harin, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da hare-haren sama da na ƙasa domin raunana ƙungiyoyin ta’addanci, kare al’ummomin da ke cikin haɗari da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.