Ƙungiyar Helpline Social Support Initiative (HSSI) ta yi kira da a kawo ƙarshen auren wuri da kuma ƙarfafa matakan kare haƙƙoƙin ’yan mata a Najeriya.
Shugabar ƙungiyar, Dakta Jumai Ahmadu, ce ta yi kiran a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Lahadi, domin bikin Ranar ’Yan Mata ta Duniya ta shekarar 2026.
Da take tsokaci kan taken bikin na bana, “A kawo ƙarshen auren wuri, a zuba jari kan haƙƙin ’yan mata”, Jumai ta ce zuba jari kan ’yan mata bai tsaya ga kare su daga cutarwa kawai ba, har da samar musu da ingantaccen ilimi, ƙarfafa musu gwiwa da kuma damar shiga harkokin shugabanci.
- ’Yan sandan Kano sun kama mutum huɗu, sun ƙwato motoci uku da aka sace
- Sojoji sun hallaka ’yan ta’addar ISWAP sama da 40 a Borno
- INEC ta musanta sanarwar bogi kan ’yan takarar gwamna a jihohi shida
Ta bayyana shirin Majalisar ’Yan Mata, wato Voice of the Girls Parliament, a matsayin wata hanya da ke bai wa ’yan mata damar bayyana ra’ayoyinsu, sanin haƙƙoƙinsu da kuma yin magana cikin ƙarfin gwiwa.
A cewarta, ya kamata kowace yarinya ta taso tana da tabbacin cewa ana daraja muryarta, ana kare lafiyarta, kuma tana da damar cimma burinta. Ta ƙara da cewa ’yan mata su samu damar kai ƙara, da neman taimako da bayar da rahoton barazana ba tare da tsoron cin zarafi ko zargi ba.
Jumai ta jaddada cewa nauyin kare ’yan mata ya rataya ne a wuyan manya da hukumomi, ba wai a ɗora musu shi kaɗai ba.
Ta kuma yi gargaɗin cewa auren wuri na iya yin mummunar illa ga lafiyar yarinya, karatunta da kuma damar da za ta samu a rayuwa ta gaba.
Shugabar HSSI ta buƙaci gwamnati, da shugabannin gargajiya da na addini, iyaye, malamai da ƙungiyoyin fararen hula da su ƙarfafa dokokin hana auren wuri, cin zarafi da amfani da ’yan mata ta hanyar da ta saba wa doka.
Ta kuma yi kira da a samar da makarantu masu aminci da sauƙin zuwa, tare da tallafi na musamman ga ’yan matan da ke cikin haɗari.
Haka kuma, ta bukaci a samar da hanyoyin bayar da rahoton cin zarafi cikin sirri domin a gaggauta taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
Jumai ta ƙara da cewa ya kamata a zuba jari a shirye-shiryen da ’yan mata ke jagoranta, da shirye-shiryen jagoranci da koyon sana’o’i, tare da sauraron ra’ayoyinsu da shigar da su cikin tsara manufofi da shirye-shiryen da suka shafe su.
Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su mayar da alkawuransu zuwa matakan da za a iya aunawa, tana mai cewa kare haƙƙin ’yan mata nauyin kowa ne a cikin al’umma.