Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta musanta wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka danganta da ita kan jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohin Zamfara, Gombe, Delta, Plateau, Yobe da Kano.
A cikin sanarwar, hukumar ta bayyana cewa ba ita ce ta fitar da bayanin ba, tare da gargaɗin jama’a da su yi watsi da shi, kada kuma su sake yaɗa shi.
- INEC ta fitar da jerin ’yan takarar gwamnan Gombe, babu sunan Pantami
- Atiku ya bukaci a ceto Ahmed Zakka, matarsa da jaririnsu da aka sace a Kaduna
INEC ta shawarci jama’a da su riƙa tantance sahihancin bayanan zaɓe ta hanyoyin sadarwarta na hukuma, ciki har da shafinta na intanet, www.inecnigeria.org, shafin Facebook mai suna INEC Nigeria, da shafukanta na X da Instagram, @inecnigeria.
INEC ta jaddada aniyarta ta samar wa jama’a sahihan bayanai kan harkokin zaɓe, tare da kira ga kowa da kowa da ya dogara da sanarwarta ta hukuma kawai domin kauce wa yaɗa bayanan ƙarya.