Ɗaliban kwas na 48 na Kwalejin Horar da Hafsoshin Sojoji ta Najeriya (AFCSC) sun ziyarci rundunar sojin Najeriya ta 11 da ke ƙarƙashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta ƙungiyar ECOWAS a Gambiya (ECOMIG), a ranar Talata, 13 ga Oktoba, 2026.
Tawagar, wadda Kwamanda Olamiju Olusegun Obasa ya jagoranta, ta kai ziyarar ne a sansanin rundunar da ke Yundum, a matsayin wani ɓangare na rangadin karatu da ɗaliban ke gudanarwa a ƙasashen Afirka.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Kwamanda Obasa ya gode wa kwamandan rundunar Najeriya ta 11, Laftanar Kanal Yahaya Mohammed Abdullahi, bisa kyakkyawar tarbar da ya yi wa tawagar.
- Gwamnatin tarayya ta goyi bayan shirin bunƙasa noma a ƙauyuka
- Likitocin haƙora sun yi tsada, abin da ke hana ’yan Najeriya samun kulawa — Likita
Ya kuma yaba masa kan jagoranci, jajircewa wajen gudanar da aiki da kuma ƙoƙarin bunƙasa rundunar.
Obasa ya buƙaci ɗaliban hafsoshin da su kasance masu ladabi, jajircewa da mayar da hankali kan aikinsu, yana mai cewa waɗannan halaye na da muhimmanci wajen ƙwarewa da ci gaban aikin soja.
A nasa jawabin, Laftanar Kanal Abdullahi ya gode wa jagororin kwalejin da tawagar bisa ziyartar rundunar, tare da yaba musu kan ƙoƙarin kiyaye ingancin horar da hafsoshin sojoji, inda ce irin wannan horo na taimakawa wajen ƙwarewar jami’an soja da kuma ɗaukaka martabar kwalejin.
Ziyarar ta bai wa ɗaliban damar fahimtar ayyukan rundunar Najeriya da gudummawar da take bayarwa wajen aiwatar da aikin ECOMIG a Gambiya.
An gudanar da bayani kan ayyukan rundunar, tattaunawa tsakanin mahalarta, musayar kyaututtuka, ɗaukar hotunan haɗin gwiwa da kuma liyafar cin abinci domin girmama tawagar.