Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Shiga da Gudanar da Kasafin Kuɗi ta Najeriya (RMAFC) ta buƙaci ma’aikatanta su ƙara ladabi, riƙon amana da nuna ƙwarewa domin inganta ayyukansu.
Shugaban hukumar, Dakta Mohammed Bello Shehu, ya bayyana hakan yayin buɗe taron horaswa kan tantance aikin ma’aikata da ladabtarwa a Abuja, wanda aka gudanar daga 13 zuwa 14 ga Oktoba, 2026.
- Likitocin haƙora sun yi tsada, abin da ke hana ’yan Najeriya samun kulawa — Likita
- Gwamnatin tarayya ta goyi bayan shirin bunƙasa noma a ƙauyuka
Ya ce tantance aikin ma’aikata na taimakawa wajen gano ƙwazon ma’aikata, inda ake buƙatar gyara da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati.
Shugaban kwamitin kula da harkokin ma’aikata, Ntufam Eyo-Nsa Whiley, wanda ya wakilci shugaban hukumar, ya buƙaci mahalarta su inganta tsarin tantance aiki da kula da bayanan ma’aikata.
Hukumar ta ce taron ya ƙunshi batutuwan tsara manufofin aiki, ladabtarwa, sadarwa da rubuta rahotanni, domin gina ma’aikata masu ƙwarewa da mayar da hankali wajen cimma sakamako.