Hoto: NAN

Gwamnatin tarayya ta goyi bayan shirin bunƙasa sarkar darajar amfanin gona (VCDP), wanda Asusun Raya Aikin Gona na Ƙasa da Ƙasa (IFAD) ke tallafawa, domin bunƙasa yankunan karkara da faɗaɗa tattalin arzikin Najeriya.

Daraktan Sashen Ayyukan Abokan Hulɗa na Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya, Dakta Emmanuel Akogun, ya bayyana hakan a taron fara aikin tawagar sa ido ta haɗin gwiwa karo na 13 tsakanin gwamnatin tarayya da IFAD a Abuja ranar Talata.

Ya ce shirin da ake aiwatarwa a jihohi tara ya mayar da hankali kan noman shinkafa da rogo, sarrafa su da kuma tallata su. Ya ƙara da cewa shirin na taimakawa wajen ƙara kuɗin shiga a fannin manoma, da rage asarar amfanin gona bayan girbi da inganta wadatar abinci.

Akogun ya ce shirin ya taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, da faɗaɗa sana’o’in masu sarrafa amfanin gona da inganta rayuwar al’ummomin karkara, musamman mata da matasa.

Ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da aiki tare da IFAD domin faɗaɗa nasarorin shirin.

Shi ma Daraktan Sashen Hulɗar Ƙasashen Waje da Tattalin Arziki na Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, Stanley George, wanda Andrew Arebun ya wakilta, ya yi kira da a gaggauta sakin kuɗaɗen shirin tare da tabbatar da biyan gudummawar da gwamnatocin jihohi suka yi alkawari a kan lokaci.

George ya ce duk da ci gaban da aka samu, har yanzu akwai matsalolin jinkirin sakin kuɗaɗe, da rashin biyan gudummawar jihohi a kan lokaci da ƙarancin ababen more rayuwa da za su jure sauyin yanayi.

Ya buƙaci a rage tsaikon gudanarwa, a ƙarfafa haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu wajen sayen amfanin gona, sannan a inganta sa ido domin tabbatar da dorewar shirin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *